Jamus za ta gurfanar da tsohon shugaban Kataloniya
March 25, 2018Talla
Tsohon shugaban yankin Kataloniya na kasar Spain, Carles Puigdemont da hukumomin Jamsu suka cafke zai gurfana a gaban kotu a wannan Litinin mai zuwa. An kama Puigdemont sakamakaon sammaci na kasa da kasa da Spain ta bayar bisa tuhumansa da laifukan tayar da tawaye.
'Yan sandan Jamus sun kama Carles Puigdemont lokacin da yake yunkurin shiga kasar daga kasar Denmak.