Tsohon shugaban Mali Moussa Traore ya rasu
September 15, 2020Traore ya dare kan karagar mulki kasar ta Mali ne shekaru takwas bayan da ta samun mulkin kai daga Faransa kuma ya samu damar hawa gadon mulkin ne a wani juyin mulki da ya yi a shekarar 1968, sannan a shekarar 1979 ya mayar da kansa shugaba na farar hula.
Moussa Traore ya bar gadon mulki ne a shekarar 1991 biyo bayan juyin mulkin da aka yi masa bayan da al'ummar kasar suka shafe kwanaki suna zanga-zanga ta adawa da mulkinsa sakamakon tabarbarewa tattalin arziki da kasar ta fuskanta a wancan lokacin.
Rasuwar tasa dai na zuwa ne kusan wata guda bayan da sojoji suka hambarar da shugaban kasar ta Mali Ibrahim Boubar Keita, wanda yanzu haka kungiyar ECOWAS ke ta fadi-tashi wajen ganin gwamnatin mulkin sojan kasar ta girka gwamnatin rikon kwarya da za ta kunshi farar hula.