SiyasaAsiya
Tsohon shugaban Philippines Duterte ya shiga komar yan sanda
March 11, 2025
Talla
'Yan sandan Philippines sun cafke tsohon shugaban kasar Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talata, bisa sammacin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kadan da saukarsa daga birnin Hong Kong.
Fadar shugaban kasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan dimbin jama'a a lokacin mulkinsa, wanda ya fake da yaki da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi.
Karin bayani:China da Philippines na nuna wa juna dan yatsa
Hatsaniya ta barke a filin jirgin saman lokacin da 'yan sanda suka kama Mr Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa hakkokinsa da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi.