Tsohon shugaban Tunisiya ya rasu
September 19, 2019Talla
Marigayi Zine El Abidine Ben Ali, ya jagoranci kasar ta Tunisiya ne a tsakanin shekarar 1987 zuwa 2011, kuma shi ne shugaban kasa na farko da aka hambarar da gwamnatinsa a guguwar juyin juya hali a shekarar 2011.
Bayan nasarar hambarar da gwamnatin nasa, hakan ya yi sanadiyar kawar da wasu shuwagabanni a yankin irin su Hosni Mubarak na Masar da kuma Moamar Gaddafi na Libiya.
A tsakiyar shekarar 2012 ne aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai sakamakon kama shi da laifin kisan masu zanga-zanga wadanda suka yi sanadiyar gwamnatinsa.
A gobe Juma'a ne za a yi jana'izar marigayi Shugaba Zine El Abidine Ben Ali, sai dai wani batu da ke daukar hankali yanzu shi ne wasiyyar da ya bayar na a binne shi a birnin Makka na kasar ta Saudiyya.