1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Zambiya na fama da rashin lafiya

June 14, 2021

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kwantar da tsohon shugaban kasar Zambiya wanda ya yi fafutukar kafa kasar Kenneth Kaunda a gadon asibiti.

Zambia ehem. Präsident Kenneth Kaunda
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Mwape

Shugaba Kaunda dai ya yi mulkin Zambiya na tsawon shekaru 27, inda ya kasance shugaban kasa na farko tun bayan da kasar ta sami 'yancin kanta daga Birtaniya a shekarar 1964.

Shugaban wanda aka fi sani da KK a lokacin shugabancinsa, ya yi matukar shahara kan sukar shugabancin wariyar launin fatar da ake yi a Afrika ta Kudu da kuma ta gwamnatin farar fata tsiraru. Sai dai daga bisani aka zarge shi da mulkin kama karya inda ya kawo tsarin jam'iyyar siyasa daya tilo.

Kaunda dai ya bukaci al'ummar kasar da sauran jama'a kan taya shi addu'ar samun lafiya, yayin da likitoci a yanzu ke kokarin ceto shi daga halin rai kwakwai mutu kwakwai da yake ciki.