1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'azzarar matsalolin rashin tsaro a Najeriya

Uwais Abubakar Idris/ ZMAJuly 3, 2015

Taron APC ya mayar da hankali kan muhimmancin jam'iyya a kan kowa, a maimakon matsalar kai sabbin hare hare da rashin tsaro da yankin Arewacin Najeriya ke fuskanta.

Niger Buhari Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

To sanin cewa tun a jawabin da ya yi na ranstuwar kama mulki shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya alkawarta shawo kan matsalar ta kungiyar Boko Haram, har ma da maimaita wannan alkawarin a 'yan kwanakin nan. Sai dai kuma a maimakon samun raguwa, ake ta fuskantar karuwar hare-hare a yanayi na ci-gaban mai gina rijiya, wannan ya sanya tambayar shin me gwamnati take yi ne a kan lamarin.

Mallam Lawali Shuaibu shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar APC mai kula da shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya.

"Abin da ka ke zato ba zai faru ba cikin kwana bakwai ko wata daya ba zai yiwu ba, barna ce aka yi aka dade ana yi, aka yi raga-raga da wani bangaren kasar nan, to ya za'a yi a ce a gyara cikin wata guda? Amma in ana son a san abin da mukama yi a duba a ga daga lokacin da muka karba me ke faruwa, ba'a ce wai ba bama-bamai ba, amma in ana son a san abin da ke faruwa a kwatanta abubuwan da suka faru a can da da na yanzu".

Hoto: Tunji Omirin/AFP/Getty Images

Taron da jamiyyar ta APC ta gudanar a Abuja dai ya tabo batutuwan da suka shafi rikicin da jamiyar ke fuskanta, musamman biyo bayan zaben shugabanin majalisar dokokin da kasar da ya bar baya da kura. Amma shugaban Najeriyar ya ce batun muhimmancin jamiyyar shi ne a gaba da komai. Na tambayi gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ko wace matsaya suka cimmawa a karshen taron na su.

"Watau da mutane suna zaton cewa bayan taron nan za'a samu matsaloli amma ina son in tabbatar maka cewa ,yanzu mun hadu yadda ya kamata kuma mun nunawa shugabaninmu muna goyon bayansu dari bisa dari, kuma maganar majalisar dokoki yanzu zamu shiga cikin lamarin za'a gyara komai ba wata matsala a jam'iyyarmu".

A yayin da ake wannan akwai kungiyar da ta gudanar da zanga-zanga na nuna bukatar gwamnatin da ma jamiyyar APC ta tabbatar da samun zaman lafiya a kasa kamar yadda ta alkawarta. Mujaheed Zaitawa jigo a kungiyar samar da ci-gaban Najeriya da suka gudanar da zanga-zangar.

Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

"Muna nuna goyon bayanmu ga jamiyyar APC bisa alkawuran da ta dauka yadda zata shawo kan harkar rashin tsaro, alkawuran da ta dauka a kan harkar ilimi, lafiya da sauransu. Wannan alkawarin da APC ta dauka ya zama dole shugaban kasa ya cika wannan alkawari ba wai rigimar da ake fama da ita a majalisar dokoki ba"

A yayin da jamiyyar APC ke kokarin shawo kan rigingimunta, abin da yafi daukan hankali shi ne yadda gwamnatin zata hanzarta shawo kan matsalar rashin tsaro da ma karuwar kai hare-hare, bisa alkawarin da ta yi daya sanya dauke cibiyar bada umurnin ta soja daga Abuja zuwa Maiduguri da ake jiran ganin tasirin yin hakan.