Tuhumar ta'addanci akan Breivik
March 7, 2012Talla
Masu gabatar da kara a kasar Norway sun tuhumi Anders Behring Breivik da laifin aikata ta'addanci da kuma kisan al'umma. A watan Yulin bara ne dai Breivik ya kai harin bam da kuma harbin kan mai uwa da wabi da yayi sanadiyar mutuwar mutane 77. Shi dai Breivik ya amsa dasa bam a wani ginin gwamnati a birnin Oslo da kuma harbin kan mai uwa da wabi akan jama'a a tsibirin Utoya.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu