1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Bikin girmama fitaccen mai hada sautuka Beethoven

September 17, 2019

Bikin tunawa da fitaccen mai hada sautuka dan asalin kasar ta Jamus mai suna Beethoven ya samu halartar kungiyar mawaka ta Take 6, 'yan asalin Afrika ta Kudu a  birnin Bonn.

Beethovenfest 2019 | Campus Konzert
Hoto: DW/P. Böll

Kungiyar mawaka ta maza zalla mai lakabin Take 6, 'yan asalin Afrika ta Kudu, inda a ci gaba da yawon zaga duniya da suke ne suka hallara a  birnin Bonn da ke kasar Jamus, inda suka baje kolin saututtuka na da da na yanzu. Sun dai bayyana a birnin na Bonn don halartar bikin tunawa da fitaccen mai hada sautuka  dan asalin kasar ta Jamus mai suna Beethoven.


Wadannan kungiyoyi biyu tare da kungiyar kade-kade ta Matasan Jamus sun hadu ne suna baja kolin fasahohinsu na wakakoki wanda ake duk shekara a birnin na Bonn. Sun yi hadin gwiwa da zimmar nuna hada  al'adun Kudancin Afirka da na Yammacin Turai.

Hoto: DW/P. Böll

Sun hada rukunan wakoki irin su jazz da pop, da RnB, da Bishara da kuma Soul da zummar assasa sautuka na kwarai na duniya, wanda suka kira kansu da sunan 'band with no instruments' wato mawaka ba tare da kayan kida ba. Sun nuna matukar farin ciki na yadda jama'a suka yaba da  wanann wakokin, wanda ba Jamusawa kadai suka yaba su ba har da 'yan kasar Rasha da suka je kafin su karaso Jamus, wanda hakan ya yi matukar ba su mamaki duba da ba su yi tsammanin hakan ba.

Hoto: DW/P. Böll

Dangane da wanann biki da 'yan kungiyar ta Just 6 suka zo a kasar ta Jamus na tunawa da Beethoven, hakan wani abin mamaki ne duba da ya akai mawaka 'yan Afrika ta Kudu suka suka san tsohon mai hada sauti a Jamus tun ƙarni na 18.

A kwanan na dai Afrika ta Kudu na cikin zafin rikicin kyamar baki da kuma cin hanci da rashawa a tsakanin magabatan kasar, kungiyar mawakan ta Just 6 ta bayyana cewar wakokinsu hanya ce ta samar da sulhu da inganta zaman lafiya. Inda suka ce a yanayin da ake ciki yanzu na wanda ya banbanta da na baya. Wakokin na ya kokarin nuna yadda jama'a za su zauna lafiya tare da juna. Waka ita ce za ta shiga ruhin mutane ta nusar da su yadda abubuwa ya kamata su kasance.