Tunawa da haɗarin Nukiliya ta Chernobyl
April 26, 2007Alumomin ƙasashen Ukrain da Rasha da kuma Belarus na bikin zagayowar shekaru 21 da haɗarin Nukiliya ta Chernobyl. A birnin Kiev Shugabar ƙasar Ukrain Viktor Yushenko ya sanya furanni domin tunawa da mutanen da haɗarin ya rutsa da su wanda ke zama haɗarin nukiliya mafi muni a tarihin duniya. Fashewar nukiliyar ya yada turiri a daíra mai yawa a faɗin tarayyar Soviet da wasu yankuna na arewacin turai. Mutane fiye da 300,000 aka tasa daga garuruwa da ƙauyuka dake kusa Chernobyl inda ƙasar Ukrain take a yanzu. An yi ƙiyasin ƙananan yara fiye da 5,000 suke ɗauke da cutar sankara sakamkon shakar gurbatacciyar iskar ta nukiliya.
Sakataren majalisar ɗinkin duniya Banki-Moon yace akwai buƙatar gamaiyar ƙasa da ƙasa su sake nazarin tallafi ga waɗannan ƙananan yara.