Tunawa da kisan kiyashi ga Yahudawa a Turai
January 27, 2013Majalisun dokokin da kungiyoyi za su yi zama a sansanonin kisan kiyashin domin tunawa da tsangwama da kuma kisan da Yahudwa suka fuskanta a fadin nahiyar Turai. Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a cikin jawabin da ta yi ta hanyar bidiyo ta nananta cewa Jamusawa sune ke da alhakin taasar da da yan Nazi suka aikata. A ranar 27 ga watan Janairun kowace shekara ne dai ake tunawa da wannan rana kasancewar a ranar 27 ga watan Janairun shekarar 1945 ne dakarun Rasha suka yantar da yahudawa a sansanonin da ake azabatar da su a garin Auschwitz dake kasar Poland. Shi dai sansanin na Auschwitz na zamam alamar tunawa da kisan kiyashi da aka yi wa miliyoyin jamaa a lokacin mulkin yan Nazi.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Saleh Umar Saleh