Tunawa da ranar mutane masu bukata ta musamman
December 5, 2019Taken bikin na bana kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shi ne ba da dama ga masu nakasa da salon jagorancinsu a matsayin daya daga cikin kudurorin muradun karni masu dorewa wanda ake sa ran cimma wa a shekara ta 2030. Manufar ware wannan rana dai ita ce tabbatar da kawar da nuna wariya ga jama'a masu bukata ta musamman din. To sai dai ko shin a arewacin Najeriya wadan nan jama'a suna samun kulawar daga hukumomi ? Kuma ko akwai wani yunkuri da kungiyoyin masu bukata ta musamman din suke yi domin tabbatar da wannan gwagwarmayar tasu, ta kai ga cimma nasara ? Wata matsala da tafi damun wannan rukuni na masu bukata ta musamman ita ce yadda wasu daga cikin al'umma ke nuna musu kyara, tsangwama tare da ganin kamar su ba mutane kamar kowa ba. Shin ko akwai wani kokari da suke yi domin wayar da kan jama'a kan wannan matsala ? To babban burin Majalisar Dinkin Duniya dai shi ne ba da dama ga masu bukata ta musamman a ko ina suke a fadin duniya a rika damawa da su a dukkan fajjojin rayuwa kasancewarsu mutane kamar kowa.