1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tuni da harin nukiliya kan Nagasaki

Ramatu Garba Baba
August 9, 2021

Japan na tuni da ranar da Amirka ta kai wani kazamin hari kan birnin Nagasaki inda mutum 70,000 suka rasa rayukansu bayan ga dubban da suka ji munanan rauni.

Japan | 75. Jahrestag des Atombombenabwurfs über Nagasaki
Hoto: Reuters/Kyodo

A wannan rana ta 08.09. 2021Japan ke tuni da kazamin harin nukiliya da Amirka ta kai kan birnin Nagasaki shekaru 76 da suka gabata. Inda mutum sama da dubu saba'in suka rasa rayukansu a yini guda. Amirka ta soma jefa makamin Nukiliya na kare dangi a birnin Hiroshima kafin ta jefa na biyun a Nagasaki, lamarin da ya sa Japan mika wuya a yayin yakin duniya na biyu. 

Duk da cewa, annobar corona ta rage wa taron da aka saba gudanarwa a duk shekara armashi, wadanda suka tsira daga harin da kuma wasu daga 'yan kasashen waje sun gudanar da addu'oi tare da yin tsit na minti guda a daidai karfe 11.02 biyu wato lokacin da Amirka ta jefa makamin karshe.


Magajin garin Nagasakin Tomihisa Taue, ya ce ya zama wajibi shugabanin kasashen duniya, sun hada kai don ganin an cimma yarjejeniyar haramta kera makaman na kare dangi. Tarihi ya nuna cewa, hare-haren na Hiroshima da Nagasaki sun kasance karon farko da ake kai hari da makami mai guba kan bil'adama a duniya.