1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara mata na fuskantar kalubale mai yawa

Zulaiha Abubakar SB
October 11, 2018

Yayin da ake tuni da ranar yara Mata ta duniya, gamayyar kungiyoyin kare martabar ilimi ta fidda sabon rahoto kan yadda hare-hare a makarantu musammam a Arewa maso gabashin Najeriya ya haifar da kuncin rayuwa.

Nigeria freigelassene Chibok Mädchen in Abuja
'Yan matan Chibok lokacin da aka karbo su daga hannun Boko Haram a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/O. Gbemiga

Yawaitar hare-hare da makami da kuma satar 'yan mata dalibai a makarantu ya kara mayar da harkar ilimin mata baya a kasashen Afrika a daidai lokacin da ake bikin ranar yara mata ta duniya. A baya-bayan nan dai gamayyar kungiyoyin kare martabar Ilimi ta fidda wani sabon rahoto daya bayyana samun hare-hare sama da 12,700 wadanda suka illata lafiyar alibai dubu sana da 21,000 a kasashen. Yayin irin wadannan hare-hare dai yara mata ne suka fi samun kansu cikin tsaka mai wuya sakamokon irin cin zarafin da suke fuskanta. Zuriel oduwole wata 'yar Afrika ce da shirya wani fim akan irin yanayin da yara mata suke ciki a Afrika bayan ta kai wata ziyarar gani da ido a kasar Ghana, inda ta bayyana abubuwan da suka ja hankalin ta:

Zuriel Oduwole 'yar Afrika wadda ta da shirya wani fim akan irin yanayin da yara mata suke ciki a AfrikaHoto: Privat

"Na ga 'yan mata sa'o'ina masu kanannan shekaru suna ragaita akan tituna mai makon ace suna makaranta don samun ilimi, don haka da na dawo daga wannan bulaguro sai na shiga nazarin wacce gudunmawa zan bayar don taimaka wa yaran nan mata su koma makarnta? wanan ce tasa a shekaru goma na fara shiri don ganin yara mata a nahiyar Afrika sun koma makaranta."

ganin yadda barazanar rashin ilimi da yaran mata ke fuskanta sakamakon kalubalen talauci, ya sanya iyaye da masu jibintar al'amuran yaran matan ke yi musu aure tun suna da kannan shekaru lamarin da a wasu lokuttan yakan janyo musu cutuka irin su yoyon fitsari ko kuma nakasa gabadaya. Zuriel ta bayyana amfani da harkar Fim a matsayin wata kafar koyar da Ilimin:

Zuriel Oduwole tare da 'yan mata 'yan makaranta a birnin Durban na Afirka ta KuduHoto: Privat

"Dauka na yi zan iya amfani da Fim a nahiyar Afrika don mata matasa su bayyana wa duniya labarin su, kuma idan ma za su iya su samu abin dogaro dakai a harkar shirya fim. Don haka nafara da kasashen Namibiya da Cote d'Ivoir da Najeriya da Habasha da Ghana da kuma Kenya, babbar nasarar da na samu ita ce daga fara wannan shiri nawa har na samu wata yarinya da ta yi wani shiri don sanar da yara irin nata labarin."

A shekara ta 2017 ne kwamitin wasu masana daga Afrika da hadin gwiwar masu rajin kare hakkin bil adama suka yi kira ga kasashen Afrika da su dauki wasu mataki don samar da daidaito tsakanin yara maza da mata a bangaren Ilimi.