Tunisa da Algeria da kuma Libya sun kafa sabuwar hadaka
April 23, 2024Kasashen Tunisa da Algeria da kuma Libya sun gudanar da wani taro irin sa na farko a birnin Tunis, da nufin samar da shawarwarin kirkiro sabuwar gamayyar jan ragamar gudanar da harkokin kula da yankinsu na Maghreb, to sai dai ba a ga kasashen Morocco da Mauritania a taron na ranar Litinin ba.
Karin bayani:An rantsar da mukaddashin shugaban kasar Tunisiya
Ministan harkokin wajen Tunisia Nabil Ammar, ya ce kasashen sun kuduri aniyar gudanar da taron a duk bayan watanni uku, don nazartar matakan tsaro a kan iyakokinsu da harkokin tattalin arziki da siyasa, da kuma duk wani sha'ani da ya shafi ci gaban kasashen uku.
Karin bayani:Zanga-zangar matasa a arewacin Afirka
Taron ya samo asali ne lokacin da shugaba Abdelmajid Tebboune na Algeria da takwaransa na Tunisia Kais Saied da kuma jagoran gwamnatin Libya Mohamed Al-Menfi suka hadu da juna, yayin taron kasashe masu arzikin makamashin Gas karo na 7 da aka gudanar a cikin watan Maris din da ya gabata a Algeria.
To sai dai Morocco ta yi shaguben cewa Algeria ta kitsa taron ne don zama kishiyarta, ta hanyar cike gurbin kungiyar hadin kan kasashen Larabawan Maghreb da aka kirkiro a Morocco a shekarar 1989.