1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kais Saied na shan suka a Tunusiya

Jennifer Holleis KK/ZMA/LMJ
February 10, 2022

Bayan rusa babbar hukumar da ke sa ido kan harkokin shari'a da kuma fuskantar zarge-zargen da ake masa na salon mulkin kama-karya, shugaban Tunusiya Kais Saied na fuskantar matsin lamba da suka da adawar cikin gida.

Shugaban kasar Tunusiya Kais Saied
Ana zargin shugaban kasar Tunusiya Kais Saied da mulkin kama-karyaHoto: Tunisian Presidency/AA/picture alliance

Ko shakka babu labarin rusa majalisar kolin harkokin shari'ar ta Tunusiya, ya zo da mamaki ga alkalan kotunan majistare na kasar 45. A cikin dare Shugaba Kais Saied ya bayar da sanarwar rusata, hakan ne ya kawo karshen aikin majalisar kolin shari'ar wanda aka kirkira a shekara ta 2016. Majalisar dai na zaman guda cikin hukumomi na karshe masu zaman kansu da ke iya yin aiki ba tare da izinin shugaban kasa mai mulki ba, kuma hakan ya kasance mataki na baya-bayan nan a jerin suka da zargi daga Saied. Tun a watan Janairu ne dai, shugaban Tunisiyan ya soke duk wasu damarmakai da ma alawus na kudi na membobin. Kafin daukar wannan mataki, Saeid ya zargi bangaren shari'a da hana gudanar da bincike kan kararrakin almundahana da ta'addanci ciki har da kisan gillar da aka yi wa wasu 'yan siyasa masu ra'ayin rikau su biyu a shekarar 2013. Zarge-zargen da majalisar ta sha yin watsi da su. A hirarsa da tashar DW Johannes Kadura da ke shugabantar ofishin gidauniyar Friedrich-Ebert a Tunisiyan, ya ce akwai alamun gaskiya a wasu batutuwan. Shugaban majalisar kolin Youssef Bouzakher ya ce za su ci gaba da gudanar da aiyukansu, domin a hukumance babu wata doka da ta isa ta rusa su. Sai dai zaman alkalan ya gagara, saboda jami'an tsaro sun tare hanyoyin zuwa harabar majalisar.

Alkalai da lauyoyi sun gudanar da zanga-zanga a TunusiyaHoto: Yassine Gaidi /AA/picture alliance

Da farko dai Shugaba Kais Saeid ya samu gagarumin goyon baya daga al'ummar Tunisiya da ke ganin zai share musu hawaye da tarin matsalolin da suke fuskanta, kuma saboda yadda ake sukar majalisar shari'ar da rashawa da almundahana ya yi fatan za a yi murna da wannan mataki. Duk da haramta zanga-zanga saboda annobar COVID-19, shugaban kasar ya umarci magoya bayansa da su fita yin gangami. Sai dai mutane kalilan ne suka amsa wannan kiran, a cewar Anthony Dworkin jami'i a majalisar Turai mai kula da dangantakar Turan da kasashen ketare. Duk da goyon bayan bangaren tsaro da yake da shi dai, manazarta na ganin Shugaba Saeid ya sake mayar da Tunisiya zamanin baya kafin lokacin juyin-juya hali sakamakon soke kundin tsarin mulki da kanannade madafun iko. Ya dai yi alkawarin nada kwamitin nazarin kundin tsarin mulkin kasar da shirya kuri'ar raba gardama kan sabon kundin a lokacin bazara, baya ga shirya zaben kasa a watan Disamba. Amma wajibi ne ya magance manyan matsalolin Tunisiyar da suka hadar da annobar corona da durkushewar tattalin arziki da uwa uba rashin aikin yi.