1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya ta bude sabon babin tarihi

December 23, 2014

Sabon zababben shugaban kasar Tunisiya ya bayyana cewa kasar za ta yi tafiya da salo irin na demokaradiyya sabanin irin na kama karya da ta sha fama da shi a shekarun baya.

Tunesien Präsidentschaftswahl 21.12.2014 - Beji Caid Essebsi
Hoto: F. Belaid/AFP/Getty Images

Sabon zababben shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi ya bayyana cewa kasar ta bude sabon feji daga mulkin kama karya da ta sha a baya inda ta dauki hanya a bisa tafarkin demokaradiyya.

Essebsi mai shekaru 88 fitacce a gwamnatocin da suka shude a Tunisiya, a jiya Litinin an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben kasar da ya kafa tarihi a kasar da juyin-juya hali a tsakanin kasashen Larabawa.

A yau Talata masu sanya idanu daga kasashen Turai za su bayyana rahotonsu kan wannan sakamakon zaben na Tunisiya inda za su bayyana cewa ko zaben ya bi duk matakan da ya kamata abi a zabukan demokaradiyya. Sai dai tuni wasu shugabannin kasashen duniya suka yaba da yadda aka yi zaben ciki kuwa har da Shugaba Barack Obama na Amirka.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo