1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya ta gargadi Turkiyya kan sa baki cikin al'amuranta

Mahmud Yaya Azare MA
April 8, 2022

Tunisiya ta yi Allah-wadai da zargin da shugaban Turkiyya ya yi mata, na "durkusar da dimokuradiyya a kasar", yadda ta dauki hakan a matsayin abin da ba za ta aminta da shi ba.

Tunesien Präsident Kais Saied
Shugaba Kais Saied na kasar TunisiyaHoto: Muhammad Hamed/REUTERS

Takun saka tsakanin kasar ta Tunisiya da Turkiyya da ke da hannun jari a kasar ta Tunisiya na biliyoyin daloli, ta faro ne tun a ranar Talata bayan da shugaban Turkiyya, Racep Tayip Erdogan, ya soki matakin da shugaban Tunisiya Kais Saied ya dauka na rusa majalisar dokokin kasarsa a makon da ya gabata.

Tuni dai shugaban na Tunisiya, Kais Saed, ya mayar da mummunan martini ga kalaman shugaban Turkiyya da ya siffanta da wani shiga sharo ba shanu cikin lamuran kasarsa.

"Mu babu wata kasar da take daukar nauyin ciyar da mu. Ba ma kuma jiran umurni daga Khalifan Daular Uthmaniya, kamar yadda muke a lokacin da suke mana mulkin mallaka.Tunisiya kasa ce mai cin gashi kanta. Babu kuma wanda ya isa ya hana yan kasarta zabin da sukaiwa kansu."

Shugaba Racep Tayip Erdogan na kasar TurkiyyaHoto: Murat Cetinmuhurdar/Turkish Presidency/Handout/AA/picture alliance

Ministan Harkokin Wajen Tunisiya Othman Al-Jarandi, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, ya tattauna da takwaransa na Turkiyya Mevlut Cavusoglu ta wayar tarho, inda ya kuma gayyaci jakadan Ankara da ke Tunisiya don nuna rashin amincewar kasarsa da kalaman na Shugaba Erdogan.

Ana dai ci gaba da mayar da martini kan wannan sa-in-sa da ke tsakanin kasashen biyu masu dasawa da juna tun bayan da Kais Saeed ya zama shugaban kasa, a lokacin da yake kawance da kungiyar Annahdha mai kishin Islama, kungiyar da ke samun goyan baya dari bisa dari daga shugaban na Turkiya, wacce rusa majalisar da kungiyar ke da rinjaye a cikin ta ya sanya ake ganin shi ne ummul haba'isin wannan danbarwar.

Baya ga Turkiyyar ma, kasashe da dama irin su Amirka da Tarayyar Turai, sun caccaki matakin rusa majalisa da shugaban na Tunisiya Kais Saed ya yi,wanda a yanzu haka shi kadai ke kidansa yana rawarsa a lamuran siyasar kasar ta Tunisiya, da a da ake buga misali da ita a matsayin zakaran gwajin dafin girka tafarkin dimukuradiyya a kasashen Larabawa, shekaru 10 da fara boren neman sauyin da ya kai ga halaka dubun dubatan mutane da raba wasu miliyoyin da mahalinsu.