1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya ta kori minista kan mutuwar mahajjata

June 22, 2024

Shugaba Kais Saied na Tunisiya, ya tsige ministan harkokin addinin kasar daga mukaminsa sakamakon mutuwar mahajjatan kasar 49 a Saudiya saboda tsananin zafi.

Shugaban kasar Tunisiya, Kais Saied
Shugaban kasar Tunisiya, Kais SaiedHoto: Chokri Mahjoub/ZUMA Wire/IMAGO

Kamfanin dillancin labaran kasar, TAP ya ruwaito cewa, Shugaba Saied ya kori Ibrahim Chaibi daga mukaminsa ba tare da wani karin bayani ba. Tuni dai Chaibi ya dauki alhakin yin sakaci a wajen sanya ido kan mahajjartan. Sai dai a cewarsa, alhazan kasar 44 daga cikin wadanda suka gamu da ajalin nasu a kasa mai tsarki, ba su yi rijistan aikin hajji ba, inda sun tafi sauke faralin ne da takadar Visar yawon bude ido.

Karin bayani:  Saudiyya ta kare mutuwar sama da mutum 1,000 saboda tsananin zafi

Hukumomin Saudi Arabiyya na cewa, yawancin mahajjatan da suka rasa rayukansu sakamakon tsanannin zafi ba su yi rijistar aikin hajji ba, wanda ya ke da matukar wuya a iya tantance adadin su ko ma gano su.

A gefe guda, gwamnatin Masar na shirin kwace lasisi tare da hukunta kamfanoni 16 da suka shirya jigilar aikin hajji bana ba bisa ka'ida ba, yayin da ake zargin yawancin wadanda suka mutu a bana, sun fito ne daga Masar.