1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Unruhen in Tunesien

February 11, 2013

Tunisiya ta faɗa cikin mummunan rikicin siyasa tun bayan kisan gillar da wasu 'yan bindiga su ka yi wa madugun 'yan adawar ƙasar Chokri Belaid.

Tunisian Prime Minister Hamadi Jebali speaks during a press conference on the result of consultations with the political parties on a government reshuffle on January 26, 2013 in Tunis. Ruling Islamist party Ennahda, first said that a reshuffle was 'imminent' last July to enlarge the current coalition that also includes two secular centre-left parties, Ettakatol and President Moncef Marzouki's Congress for the Republic. AFP PHOTO / FETHI BELAID Sufi leaders soretent the mausoleum of Sidi Bellahsen Chadly after having completed their weekly ritual on January 26, 2013 in Tunis. The Tunisian government has promised to day measures 'emergency' to protect Sufi shrines covered by dozens of attacks, an announcement Saturday called 'positive' by the Union but tradive Sufi Tunisia accuses Salafi factions of these rampages . AFP PHOTO / FETHI BELAID (Photo credit should read FETHI BELAID/AFP/Getty Images)
Hamadi Jebali Firaministan Tunisiya na EnnahdaHoto: AFP/Getty Images

Tunisiya da ke matsayin zakaran gwajin dafin guguwar juyin juya hali da ta ɓarke a wasu ƙasashen larabawa ta sake tsunduma cikin wani hali na rashin tabbas, wanda ga alamu ka iya kai ƙasar ga junin juya hali na biyu.Duk da zaɓen da ƙasar ta yi nasara shiryawa, wanda kuma ya baiwa jam'iyar Ennahda mai radin kare addinin Islama nasara, mulkin ƙasar ke ci gaba da tangal-tangal.Har yanzu majalisar rubuta kudin tsarin mulki da aka girka, ta kasa samar da cikkaken daftari wanda Tunisiya za ta yi dogaro da shi, domin girka tafarkin demokraɗiyya, da kyautata rayuwar al'umominta.

Rikicin ya ƙara rincaɓewa tun bayan hallaka Chokri Belaid ɗaya daga masu mummunar adawa da gwamnati.

A cewar Berny Sebe, malami a jami'ar Birminghan,wannan hali na gaba kura baya sayaki, da Tunisiya ta tsincin kanta ya samo asuli da ga rashin sanin makamar mulki na jam'iyar Ennahda:

Hoto: Reuters

"Jam'iya mai mulki ta Ennhada, ta kasance tamkar a aska mai baki biya.A yayin da a hannu ɗaya take buƙatar kwaikwayon sallon mulki irin na ƙasar Turkiyya na ta hanyar sasaucin ra'ayi, a ɗaya hannun kuma a fakaice ta na bada goya bayan baya ga magoyan bayanta masu tsatsauran ra'ayin addinin Islama.Ta kasa magance matsalar take haƙƙoƙin bani Adama, da kuma barazanar ga 'yan salafiya ke yi ta hallaka duk wanda ya baiyana adawa da gwamnati."

'Yan Tunisiya sun kyautata zaton al'amura za su cenza bayan kifar da mulkin tsofan shugaban ƙasa Zin El-Abedine Ben Ali,da suka yi zargi da almubazaranci da kuma handame kuɗin ƙasa, to saidai a cewar Mabrouka Khedir 'yan jarida a Tunisiya murna ta koma ciki:

"Matsalolin tattalin arzikin sune a zahiri suka addabi Tunisiya kamin juyin juya hali, kuma har yanzu a na nan dai gidan jiya noman goje, babu abinda ya cenza.Gwamnati ta kasa samo hanyoyin magance matsalolin zaman kashe wando da ya addabi kashi 20 cikin ɗari na matasan ƙasar."

A halin da ake ciki kuma yanzu ita kanta jam'iyar Ennahda mai mulki ta na fuskantar mummunar ɓarakar tsakanin masu matsanancin ra'ayi da masu ra'ayi mai sassauci ,kamar shi kansa Firaminista Hamadi Jebali, wanda ya bukaci girka gwamnatin haɗin ƙasa, wadda za ta ƙunshi masu ilimi zalla, to saidai wannan bukata ta ci karo da fushin jam'iyarsa ta Ennahda.Amma da dama daga 'yan Tunisiya sun nuna goyan baya ga Firaminista game da batun girka sabuwar gwamnati.Ahmed wani mazaunin birnin Tunis na daga masu wannan ra'ayi:

Moncef MarzoukiHoto: picture alliance/abaca

Ta makata su duka su sauka,domin ba su tsinana komai ba, babu wani cigaban da ƙasa ta samu sai ma koma baya,ta kamata su kauce su ba wasu wuri, suma a ga kamun ludayinsu.".

Ita ma dai jam'iyar CPR ta shugaban ƙasa Moncef Marzouƙi mai ƙawance da Ennhada, ta buƙaci a garambawul ga gwamnati, idan kuma haƙarta ba ta cimma ruwa ba, jam'iyar ta yi barazanar raba gari da Ennahda.

Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Halima Balaraba Abbas