1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

D China Berlin

June 29, 2011

Dangantakar China da Jamus ta kara karfi ta hanyar samun ganawar farko tsakanin majalisun ministocin kasashen biyu a birnin Berlin

Shugaban gwamnati Angela Merkel da bakon ta PM China Wen JiabaoHoto: dapd

Bisa al'ada, Jamus takan gudanar da shawarwari na gwamnatoci tsakanin ta da kasashe da take da dangantaka ta kurkusa ne dasu. China tana daya daga cikin irin wadannan kasashe, saboda haka ne a birnin Berlin, karon farko aka sami ganawa tsakanin majalisun ministocin kasar ta China da Jamus. Daga baya, shugaban gwamnati, Angela Merkel tayi magana game da wani sabon shafi a dangantaka tsakanin kasar ta Jamus da China. Umaru Aliyu yana dauke da karin bayani.

A bayan yabo mai yawa ga matsayin kyakkyawar dangantaka tsakanin Jamus da China, shugabannin kasashen biyu sun tabo wani al'amari mai sarkakiya a lokacin da suka baiyana gaban manema labarai. A daidai lokacin da shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta tabo batun kare hakkin yan Adam, sai bakon ta, Pirayim ministan China Wen Jiabao na'urar dake masa fassarar abin da ta fada ya sami tangarda. Shugaban gwamnatin daga baya ta sake maimaita farin cikin ta a game da matakin da China ta dauka na sakin yan adawa, Ai Wei Wei.

Tace mun kuma nunar da cewar yana da muhimmanci duk irin shari'ar da za'a yiwa Ai Weiwei ya kasance an yi ta ne a bainar jama'a, kamar dai yadda duk shari'ar da za'a yiwa sauran wadanda ake zargin su da laifukan adawa da gwamnati an baiwa bainar jama'a damar fahimtar ta.

Angela Merkel da Wen Jiabao da ministan tattalin arzikin Jamus Philipp RöslerHoto: picture alliance/dpa

To sai dai duk da banbancion ra'ayi kan batun kare hakkinyan Adam, tuntubar juna ta farko tsakanin majalisun ministocin kasashen biyu ta maida hankali ne kan batun tattalin arziki, inda aka sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin kai a fannonin ciniki da fasaha da aiyukan bincike. Pirayim ministan China, Wen Jiabao yace zurfin ci gaban da tattalin arzkin Jamus yake dashi, ya burge ni matuka, inda saboda haka ne tawagar sa tayi odar kayaiyakin masana'antu na Jamus masu yawan gaske. Haka nan kuma kamfanonin kera motocin Jamus na Volkswagen da Daimler da kamfanin magunguna na BASF, sun sami izinin kakkafa sabbin rassan su a kasar ta China.

Yace tuntubar juna ta farko tsakanin gwamnatocin China da Jamus ta sami matukar nasara kuma an tafiyar da ita sosai yadda ake bukata. Wannan dai shine karo na farko da ministoci 13 suka yi mani rakiya a wata ziyarara. Mun sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin kai da na ciniki da harkokin kasuwanci har kimanin 20, bisa adadin kudi dollar miliyan dubu 15.

Shugabannin kasashen biyu sun kuma tabo halin da kudin Turai na Euro yake ciki a yanzu da kokarin da nahiyar take yi na shawo an wahalolin dake tatare dashi. Dangane da haka, shugaban gwamnati, Angela Merkel tace:

Neman yadda za'a shawo kan rikicin kudin Euro na TuraiHoto: dapd

Babu shakka mun kuma duba halin da Euro yake ciki kuma ina matukar farin cikin ganin cewar Pirayim minista Wen Jiabao ya maimaita muhimmanci da darajar da ya dorawa kudin na Euro, ya kuma nuna sha'awar sa a game da hana fadi-tashin kudin na Euro. Ni a bangare na, na tabbatar da cewar Jamus zata yi iyakacin kokarin ta domin ganin cewar kasashe masu amfani da Euro din basu sami koma baya ba, amma a maimakon haka, sun ci gaba da nunawa junan su zumunci a wannan lokaci mai wahala.

Pirayim minista Wen Jiabao yace kasar sa zata bada gudummuwa domin taimakawa kokarin da ake yi na shawo kan matsalolin da Euro din yake fama dasu yanzu, alal misali ta hanyar sayen hannayen jari na kasashen Turai. Yace a kasuwnanin duniya, samun yarda da juna darajar sa tafi zinariya. Wannan jawabi ne da ya nunar da kyakkyawar yanayin da aka samu, lokacin ganawar ta farko ta gwamnatocin Jamus da China a Berlin.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Muhammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani