1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kafa sabuwar gwamnati a Tunusiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 12, 2021

Shugaba Kais Saied na Tunusiya ya sanar da shirinsa na kafa sabuwar gwamnati, tare da bayyana cewa za a yi gyara ga kundin tsarin mulkin kasar.

Tunesien I Präsident Kais Saied
Shugaba Kais Saied na TunusiyaHoto: Slim Abid/AP/picture alliance

Sanarwar ta Shugaba Kais Saied na zuwa ne, makonni bayan da ya kori firaministansa tare da dakatar da majalisar dokokin kasar, a wani mataki da masu sukarsa suka bayyana da juyin mulki. A wani jawabi da ya yi a wasu gidajen talabijin biyu na Tunusiyan, Shugaba Saied ya ce zai sanar da sabuwar gwamnatin nan ba da jimawa ba. A cewarsa zai zabi mutannen da ya tabbatar suna da gaskiya da rikon amana, sai dai bai bayyana takamaiman lokacin da zai yi nadin ba. Saeid dai na shan matsin lamba kan bukatar kafa gwamnatin, musamman daga kasashen yamma da ya ce ba ya bukatar suna tsoma bakinsu a lamuran kasarsa.