1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar mata a majalisar Tunusiya

Gazali Abdou Tasawa
November 13, 2019

A kasar Tunusiya daruruwan mata ne suka gudanar da zanga-zanga a wannan Laraba a gaban majalisar dokokin kasar domin nuna rashin amincewarsu da wani dan majalisar dokokin kasar da ake zargi da cin zarafin mata.

Tunesien | Proteste für Frauenrechte
Hoto: Getty Images/AFP/F. Belaid

A ranar 11 ga wannan watan Oktoban da ya gabata ne dai wani faifayen bidiyo da ke nuna dan majalisar mai suna Zoubeir Makhlouf na istimna'i wato wasa da al'aurarsa ya yadu a saman shafukan sada zumunta tare da haifar da muhawara a kasar.

 An dai gurfanar da dan majalisar a gaban wata kotun birnin Nabeul a ranar 14 ga watan na Oktoba, amma kotun ta sallame shi bayan da ya bayar da uzurin cewa yana fitsari ne kawai da ya kasa rikewa a sakamakon cutar siga da yake fama da ita, kana yana da rigar kariyarsa ta dan majalisa.

 To sai dai a loakcin bikin bude zaman majalisar a wannan Laraba matan suka fantsama a gaban harabar majalisar domin neman ya fice daga cikin majalisar ya kuma sake gurfana a gaban kuliya a bisa zargin cin zarafin mata.