Kyautar Nobel ga Tunusiya
October 9, 2015Kungiyoyin dai sun hadar da kungiyar 'yan kwadagon kasar da gamayyar lauyoyi gami da kungiyar masu masana'antun hannu sai kuma kungiyar kare hakkin dan Adam. Wadannan kungiyoyi dai a shekara ta 2013 dai-dai lokacin da kasar ke fuskantar kashe-kashen kusoshin kasar da yamutsin siyasar da ya kama hanyar jefa ta cikin yakin basasa, sun yi tsayiwar daka wajen tilasta wa bangarori masu gaba da juna zaman kan teburin shawara. Kungiyoyin sun kuma ci gaba da bibiyar taron da ya kai ga shirya sahihin zabe da warware matsalolin kasar a siyasance bisa tsarin kare 'yanci da hakkokin jinsi da ra'ayin addini. Reemah Zahran kusa a gamayyar shirya taron kasar na Tunusiya kuma mamba a kungiyar lauyoyin kasar ta ce wannan kyauta jinjina ce ga yin riko da halin ya kamata da danne zuciya a dai-dai lokacin da idanu suka rufe saboda fushi.
Murna tamkar ranar haihuwa
"Kai ka ce yau aka haife mu don murna. Samun wannan lambar ya yi matukar mana bazata. Wannan kyauta ce ga nuna halin dattaku, kyautace ga Tunusiya da ma duniyar zaman lafiya. Fatanmu kasashen duniya su yi riko da irin wadannan matakan da muka dauka wajen warware rikita- rikitar siyasa a ko ina."
Shi ma shugaban kasar ta Tunusiya Beji Caid Essebsi wanda aka ya dare kan karagar mulki a zaben da biyo bayan tattaunawar, ya ce wannan kyauta wata izina ce ga 'yan siyasar kasar baki daya.
"Ina taya wannan kwamati murna da kuma illahirin jam'iyu da kungiyoyin da suka amince suka shiga tattaunawar da wannan kwamati ya tsara, domin da basu amince da hakan ba da ba a cimma tsara kundin tsarin mulki da gudanar da zabe ba. Wannan lamba hannunka mai sanda ce ga 'yan siyasa kan cewa muci gaba da rungumar juna, masu ra'ayin Islamarmu da 'yan gurguzu da masu raba addini da mulki da masu sassaucin ra'ayi da ma masu matsanancin ra'ayi.
Kasantuwar cewa wannan shi ne karo na hudu da kasashen Larabawa ke samun wannan kyauta kuma kasancewar kungiyoyin hudu sun fafata ne da 'yan takara kimanin 273 da ke neman lashe lambar, ya sanya al'umomin kasashen Larabawan sake farfado da fatansu na samun nasarar juyin- juya halin da a kai masa rubdugu ake neman murkushe shi.
Kasar da juyin-juya hali yai nasara
Tunusiya dai ita ce kasa daya tilo da ta kai labari daga cikin kasashen da guguwar juyin-juya halin na kasashen Larabawa ya kada cikinsu, wannan lambar girmamawa sako ne da ke sanar da al'ummar kasashen Larabawan cewa muddin suka hade kansu su kai hakuri da juna, to lalle za su yi nasara.
Baki daya dai 'yan kasar ta Tunusiya na fatar wannan lambar girma ta kasance sako ga kasashen duniya da su daina yin dari-dari wajen batun sanya hannayen jari ko kulla huldodin diplomasiyyar da za su taimaka wa tattalin arziki a Tunusiya domin dorewar tsarin mulkin dimokiradiyya a kasar.