1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu na tunanin janye dokar shari'a

Abdourahamane Hassane
March 27, 2023

Majalisar Wakilan Cibiyoyin Yahudawa da ke a Faransa (CRIF) ta yi kira ga gwamnatin Isra'ila da ta dakatar da shirinta na yin gyaran fuska ga tsarin shari'ar kasar.

Masu adawa da yi wa bangatren sharI'a Kwaskwarima a Israila
Masu adawa da yi wa bangatren sharI'a Kwaskwarima a IsrailaHoto: Ammar Awad/REUTERS

 

Hakan na zuwa daidai lokacin da babbar kungiyar kwadago ta kasar ta kira wani babban gangami tare da yajin aiki na gama gari, domin kara nuna adawa ga dokar da ke kara karfin iko ga zababun kasar fiye da alkalai.Tun farko shugaba Isaac Herzog ya yi kira ga gwamnati shima da ta gaggauta dakatar da sake fasalin bayan da aka kwashe daran jiya ana shan arangama tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sanda a birnin Tel aviv. Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce ana sa ran firaminista Benjamin Netanyahu, zai yi magana a bainar jama'a kuma mai yiwuwa ya amince da dakatar da kwaskware dokar shariar. Watannin ukuke nan da ake gudanar da zanga-zanga a Isra'ilan a kan wannan shirin doka.