1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Covid-19: Duniya za ta fara rarraba rigakafi a Disamba

November 20, 2020

Kamfanonin BioNTech na Jamus da Pfizer na Amirka wadanda suka sanar da samo rigakafin coronavirus sun sanar da cewa akwai yiwuwar za a fara rarraba rigakafin nan da wata mai zuwa.

Symbolbild I Impfstoff Coronavirus
Hoto: David Cheskin/PA/picture-alliance

Kamfanonin sun ce suna dab da samun amincewa ta karshe daga hukumomin Amirka da Tarayyar Turai bayan da suka gano rigakafin wace suka ce tana bayar da kariyar kaso 95 cikin 100 na hadarin kamuwa da corona.

Wannan na zuwa ne a yayinda a Jumma'ar nan MDD ta yi gargadi ga likitocin da ke amfani da maganin Remdesivir wurin warkar da cutar corona. Masu bincike a hukumar lafiya ta duniya sun ce hakika maganin yana da wasu alfanu, amma babu wani tartibin bayanin da zai nuna cewa maganin zai kawo wa masu corona mafita.