Rasha ta amince da 'yancin 'yan awaren Ukraine
February 22, 2022Sai dai martanonin da suka biyo bayan matakin na Rasha sun sha bamban daga kasashen yammacin duniya da wadanda ke goyon bayan Vladimir Putin.
Dokokin biyu ne shugaban na Rasha Vladimir Putin ya sanya wa hannu domin amincewa da 'yancin cin gashin kan jamhuriyoyin Donetsk da Lugansk. Tuni ma ya umarci sojojin Rasha da shiga yankunan 'yan aware a gabashin Ukraine bayan amincewa da su domin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya.
A cikin wani dogon jawabi da ya yi ta gidan telebijin inda ya bayyana fushinsa, Mr. Putin ya bukaci Ukraine da ta gaggauta dakatar da matakin soji kan 'yan awaren, idan ba ta so a ci gaba da zubar da jini. Ita dai kasar Rasha ta jibge dakaru kusan 150,000 a kan iyakokin kasar Ukraine, lamarin da ke kara nuna fargabar wani gagarumin farmaki.
Vladimir Putin ya ce: " A karkashin manufofin Bolshevik ne aka samar da Ukraine ta Tarayyar Soviet ta tashi, wanda ko da a yau ake kira "Ukraine kamar yadda Vladimir Ilyich Lenin ya rada mata." Shi ne ya kafa ta kuma ya zana tasawirarta. An tabbatar da wannan a karkashin takaddun adana bayanai, ciki har da Donbass. Amma yanzu ana rusa abubuwan tunawa da Lenin a Ukraine. Wannan shi ne abin da suke kira rabuwa da mulkin gurguzu? A shirye muke mu nuna muku ainihin abin da ake kira manufofin gurguzu a Ukraine."
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tir da abin da ya kira tauye hakkin kasar Ukraine ta hanyar raba ta gida biyu, wanda bai dace da dokokin kasa da kasa ba. A nashi bangaren Sakatare-Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya yi amfani da kakkausar murya wajen bukatar Rasha da ta zabi hanyar diflomasiyya wajen yayyafa ruwan sanyi a takaddamar da ke tsakaninta da ukraine, tare da ta janye sojojinta kamar yadda ta yi wa kasashen duniya alkawuri. Amirka kuwa a ta bakin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ta ce Rasha ta cancanci martani mai tsauri kuma cikin gaggawa.
Ita kuwa Kungiyar Tarayyar Turai EU ta sha alwashin ladabtar da wadanda ke da hannu a wannan haramtacciyar doka, wacce a cewarta ta saba da yarjejeniyar Minsk. Tuni ma kantomar harkokin wajen EU Josep Borrell ya ce Kungiyar Tarayyar Turai za ta yanke shawara a wannan Talata kan takunkumai na farko da za a kakaba wa Rasha bayan amincewar da Moscow ta yi na ‘yancin Donetsk da Lugansk.
"Babu shakka, wannan martanin zai kasance ta hanyar sanya takunkumi, anda ministoci za su ba shawarar abin da ya kamata a yi. Kamar yadda kuka sani, a cikin tsarin hukumomin Tarayyar Turai, Hukamar zartarwa ne ke da hurumin yanke shawarar takunkumin da aza a aza a karkashin shawarar babban wakilin, wanda a fili yake aiki tare da shugabancin karba-karba na Tarayyar Turai. Kuma dole ne a yi magana da yawu daya. . Wannan ba yana nufin cewa a yau za mu dauki dukan takunkuman ba ne. Za mu dauki matakai ne na gaggawa, wannan martani ne cikin sauri."
Sai dai Siriya da ke kawance da Putin ta goyi bayan matakin na Rasha kuma ta ce za ta yi aiki tare da jamhuriyar Donetsk da Lugansk, a cewar ministan harkokin wajen kasar Fayçal al-Meqdad. Ita ma Chaina da ke dasawa da Rasha ba ta fito karara ta la'anci matakin da Rasha ta dauka ba. Maimakon haka ma ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a rikicin na Ukraine da su kai hankali nesa tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya haifar da tashin hankali. Ga ma abin da Wang Wenbin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ke cewa
"Kasar Sin ta damu da halin da ake ciki a Ukraine. Matsayinmu kan batun Ukraine bai taba sauyawa ba: ya kamata a mutunta matsalolin tsaro na kowace kasa. Ya kamata a kiyaye manufofi da ka'idojin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa. Takun sakar Ukraine na da nasaba da jinkirin aiwatar da sabuwar yarjejeniyar ta Minsk."
Sai dai Moscow ta tabbatar da cewa kofofinta a bude a fanin diflomasiyya don samar da maslaha. Ita kuwa gwamnatin Ukraine ta yi kira ga kasashen yammacin duniya da su dauki tsauraran takunkumi kan kasar Rasha, bayan da ta amince da ‘yancin cin gashin kan yankunan kasar biyu masu goyon bayan Rasha.