1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Rufe wuraren shakatawar jama'a da wuri

Zainab Mohammed Abubakar
March 16, 2020

Mahukuntan Jamus na shirin rufe wuraren dandazon jama'a don shakatawa da suka kunshi shaguna da wuraren shakatawa da na kallon kayan tarihi, saboda karuwar yaduwar cutar Coronavirus.

Deutschland Berlin 2011 | Hackesche Höfe & Restaurants
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Kalaene

Ofishin shugabar gwamnati Angela Merkel ya gabatar da jerin wuraren da irin wannan matakai suka kunsa, wanda jihohin kasar 16 suka amince da su, tare da aiwatarwa ba tare da bata lokaci ba. 

 Kasashe akalla guda 7 a cikin 27 da ke kungiyar Tarayyar Turai ta EU suka sanar da rufe iyakokinsu kawo yammacin yau Litinin saboda fargabar yada cutar Corona.
Tuni dai wasu yankuna kasar suka sanar da manufar daukar akasarin wadannan matakai da gwamnatin tarayyar ta gabatar. Sauran wuraren da dokar zata shafa sun hada da Choci-choci, da masallatai da sauran wuraren bauta na Yahudawa da makamantansu. 

Hoto: AFP/T. Schwarz

Jamus ta zama kasa ta baya-bayan nan da ta rufe iyakokinta saboda annobar cutar Coronavirus a nahiyar Turai. Kasar dai ta bi sahun kasar Italiya ne wace cutar Coronavirus tafi yi wa illa, abin da ya sa ta rufe kasarta ba-shiga-ba-fita.

A hukumance Jamusawa da wasu kayayyaki masu muhimmanci kamar magunguna kadai aka bari su iya ketarowa kasar.

Tun da farko dai Ministan harkokin cikin gida, Horst Seehofer ya ce wannan mataki ba shi ne na karshe ba a jerin matakan da Jamus ta shirya dauka don dakile yaduwar cutar Coronavirus.

'' Wannan cuta ta Corona na yaduwa tamkar wutar daji. Daya daga cikin matakan da muke ganin sun dace shi ne dod'e hanyoyin da cutar ka iya bazuwa. Wannan yana da muhimmanci''

Hoto: epd/O. Dietze

Alkaluma na baya-bayan nan dai na nuna cewa akwai mutane kusan dubu biyar da suka kamu da cutar Corona a nan Jamus, daura da wasu 12 da suka rasa rayukansu.

Ana fargabar matakin rufe-rufen da wasu kasashen Turai ke yi zai shafi mutum milyan 1.5. Sai dai ga Osteriya wacce Jamus ta rufewa boda  ta ce, kawo yanzu ba ta kai ga ta rufe wa makwabtanta kofa ba. Amma za su ci gaba da daukar matakai a cikin gida don dakile yaduwar cutar ta Corona wace ta fara yin karfi a kasar.  Sebastian Kurz shi ne shugaban gwamnatin ta Osteriya.