Shekaru 75 da gama yakin duniya na biyu
May 8, 2020An dai gudanar da bikin na bana cikin halin taka tsan-tsan sabanin yadda aka saba gudanarwa a baya, sakamakon annobar coronavirus. Ga misali a nan Jamus, shugabar gwamnati Angela Merkel da shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier sun ajiye filawoyi a wajen tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin, inda suka bi matakan bayar da tazara da gujewa cunkoso da yanzu haka ake bi a kasar, domin dakile yaduwar annobar coronavirus din.
Hitler ya bayar da kai
A ranar 30 ga watan Afrilu da rana tsaka, Adolf Hitler ya ga cewar hanya daya ce kawai mafita. Dakarun Tarayyar Soviet sun afkawa tsakiyar birnin Berlin. Hitler dai ya ji tsoron fadawa hannunsu a raye, saboda irin ta'asar da yayi. Nan take jagoran kama karyar na 'yan Nazi da sabuwar amaryarsa ta yini guda Ever Braun suka harbe kansu, a wani dakin karkashin kasa da ke fadar mulki ta Reich Chancellery da ke Berlin. Daga bisani sauran mabiyansa suka kone gawarsa, sannan suka binne tokar a kusa da kofar ginin.
To amma sai a ranar takwas ga watan Mayu ne aka kawo karshen daular Hitler a hukumance, aka kuma sa jami'an gwamnatin Jamus din ta waccan lokaci suka rattaba hannu domin mika wuya ba tare da wani sharadi ba. Da haka yakin duniya na biyu ya kawo karshe a nahiyar Turai, wanda ya fara da mamayen da Jamus ta yi wa Poland a ranar daya ga watan Satumba na 1939. Sai dai an ci gaba da gwabza yaki a watannin da suka biyo baya a yankin Asia, kafin Japan ta mika wuya a ranar biyu ga watan Satumbar 1945.
Cin galaba ko 'yantarwa?
Yawancin biranen Jamus sun koma kamar kango. Kasar da ke da alhaki ba wai farkon yakin ba, har ma da kisan kare dangi da nuna wariyar launin fata a sansanonin da aka garkame mutane. Su kuma Jamusawa fa ya ya suke ji? An samu galaba a kansu ne ko kuma an cetosu daga mulkin Nazi? Fitaccen dan siyasa daga Jami'yyar SPD Egon Bahr a wata muryarsa da aka nada kuma ake ajiye da ita a gidan adana kayan tarihi da ke Bonn ya ce: "Jim kadan bayan takwas ga watan Mayu, ban yi tunanin ko an 'yanta mu ko kuma an samu galaba akanmu ba. Tabbas an ci nasara a kanmu, sai kuma me, an kuma 'yantar da mu. Duka biyun sun faru. A wurina duk daya ne. Kasancewar muna raye. Har yanzu muna raye. Shi ne abun da ke da muhimanci.
Yawancin wadanda suka tsira daga yakin, tunaninsu kusan daya ne da na Bahr. Sai dai mafi akasari su na cikin wani yanayi na gigita da dimuwa: Maza saboda fafatawa a filin daga, mata kuwa kimanin dubu 800 zuwa miliyan biyu saboda fyade, musannan daga sojojin Tarayyar Soviet, duk da cewar a yanzu haka dai babu takamaiman alkaluman da ke nuna yawan matan.
An samu saukin al'amura
A hirar da tashar DW ta yi dashi, masanin tarihi kuma mai sharhi kan al'amura Frorian Huber ya ce, idan ana magana tsakanin shekarun 1945 zuwa 1949, akwai abubuwa biyu da suka nunar da muhimmancin wannan lokacin: "Na farko, dole ne Jamusawan su amince da cewar an ci nasara akansu, wanda ya zamo abu mawuyaci ne mafi yawansu su yarda. Abu na biyu kuma, wajibi ne su shirya fuskantar sabon babin rayuwa a matsayin kasa da kuma a siyasance. A dangane da haka, lokacin da aka fara yakin cacar baka, a fili take cewar za a samu yankuna biyu har da tsarin mulki biyu, wanda zai bar tabo ga al'ummar Jamus har zuwa karshen karni."
Sai dai a cewar masanin tarihi Huber yanayin da kasar ta tsinci kanta ciki a wannan lokacin, ya saukaka al'amura musamman a yankin Jamus ta Yamma. Kazalika wajen rungumar sabon kundin tsarin mulkin kasar kamar yadda ake dashi yanzu.