Shugabannin Jamus za su shimfida furanni
May 8, 2020![Pieta Mutter mit totem Sohn Neue Wache Berlin](https://static.dw.com/image/53283763_800.webp)
Talla
Nan gaba kadan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier za su ajiye furanni a Neue Wache, dandalin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu da danginsu yayin yakin duniyar na biyu gabanin jawabi na musamman daga shugaban tarayyar ta Jamus.
Batun kebe rana ta musamann a Jamus don tunawa da yakin da ya haifar da asarar rayukan sama da mutane miliyan 50 na cigaba da fuskantar muhawara a Jamus.