SiyasaTurai
Turai ta yi fushi da China kan daure 'yar jarida
December 29, 2020Talla
Sanarwar ta EU din ta wannan Talata ta kuma bukaci China ta sako wasu karin 'yan jarida da lauyoyi da kuma 'yan fafutuka da kasar ke tsare da su.
Mai magana da yawun bangaren huldar jakadanci na kungiyar ta EU Peter Stano ya ce kungiyar ta samu bayanin da ke cewa ana gasawa 'yar jarida Zhang aya a hannu a zaman da take yi a hannun hukumomi.
A ranar Litinin ne dai China ta zartawa da 'yar jaridar hukuncin daurin shekaru hudu saboda kawo labarai masu rudani a lokacin annobar corona a Wuhan.