1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
FasahaTurai

Turai ta harba tauraron Galileo zuwa sararin samaniya

December 17, 2025

Kungiyar Tarayyar Turai ta harba tauraron dan Adam na Galileo guda biyu zuwa sararin samaniya, karo na farko tun shekarar 2018.

Harba tauraron na  Ariane 6 na zuwa ne shekaru bayan dogaro da Rasha wajen wannan aikin
Harba tauraron na Ariane 6 na zuwa ne shekaru bayan dogaro da Rasha wajen wannan aikinHoto: Ronan Lietar/AFP/dpa/picture alliance

An kaddamar da tauraron ne da safiyar Laraba ta hanyar kumbon Ariane 6 daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Kourou a tsuburin French Guiana da ke yankin Amurka a karkashin ikon Faransa . Kumbon na Ariane 6 ya fara aiki ne a bara, bayan nasarar da tsohon kumbo na Ariane 5 da aka harba zuwa tauraron dan Adam a 2018 ya samu.

Sabon harba kumbon da aka yi na nuni da kokarin Turai na dogaro da kanta, bayan da a baya ta rika amfani da kumbon Amurka da Rasha. Tsarin tauraron dan Adam na Galileo shi ne tsarin kewayen duniya na Turai, wanda aka kirkira domin rage dogaro da tsarin GPS na Amurka.

Da wannan kaddamarwa, adadin tauraron Galileo da ke zagaye duniya ya kai 24. Kamfanin Jamus na OHB ne ya kera tauraron, lamarin da jami'an Jamus suka ce zai kara daidaito da karfin tsarin tauraron da Adam na Turai.

An kaddamar da tauraron ne da safiyar Laraba ta hanyar kumbon Ariane 6 daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Kourou a tsuburin French Guiana da ke yankin Amurka a karkashin ikon Faransa. Kumbon na Ariane 6 ya fara aiki ne a bara, bayan tsohon kumbo na Ariane 5 da aka harba zuwa tauraron dan Adam a 2018.