1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rashin ruwa a Turai: Dalilai da mafita

Rangel Aguilar LMJ
September 2, 2025

Kasashe da dama a Turai na kara kokawa da karancin ruwa. Canjin yanayi, tsofaffin ababen more rayuwa, da karuwar amfani na dagula al'amura.

Fari a Spain
Fari a SpainHoto: Emilio Morenatti/AP/dpa/picture alliance

Biratnaiya ta yi fice a fannin yanayin ruwan sama a koda yaushe, sai dai kuma tana cikin kasashen da a yanzu suke fuskantar karancin ruwan. Ana samun karancin ruwan sama da tsananin zafi da kuma karuwar bukatar ruwan, abin da ke kara lalata al'amura.

Idan aka fuskanci fari mai yawa duka  wuraren da ake dana ruwan suna kasancewa a bushe, abin da ke nufin bukatar adana ruwan sosai. Mike Muller kwararren injiniya ne a fannin ruwa, kana malami a makarantar Wits da ke bayar da horo a kan harkokin mulki a Afirka ta Kudu ya nunar da cewa:

Kankara ta narke a Obergoms a SwitzerlandHoto: Arnd Wiegmann/REUTERS

"A yanzu an rage ruwan da ake bai wa gidaje miliyan daya, sabo da mai? Saboda babu isasshen ruwa a wuraren adana shi. Saboda mai?  saboda ya yi karanci.

"Adana ruwa abu ne mai kyau, sai dai matsalar da zai magance na da iyaka. Lokacin fari a nan gizon ke saka, domin iya inda ruwan da aka tara zai gaza ke nan. Mun fahimci cewa yana da muhimmanci a yi amfani da yankunan da suke da yawan ruwa, a kai ruwan ga yankunan da bai ishe su ba. Masana a kan muhalli suna adawa da hakan, amma in aka yi la'akari da illar da karancin ruwan ke yi ga al'umma da ma tattalin arziki za ka fahimci yadda matsalar ke shafar su."

Marseille da ke a FaransaHoto: Andia/imago images

Ba dai a Birtaniya kadai ake samun wannan matsalar ba, kamar yadda kwararre a fannin ruwa a cibiyar kula da muhalli ta Turai Sergiy Moroz ya nunar yana mai cewa:

"Ruwa ya zama abu mai muhimmanci, a kasashe da dama na kungiyar tarayyar Turai ana fuskantar matsaloli dabam-dabam. A bayyane yake, saboda ba a kula da harkar ruwan yadda ya kamata. Sai kuma matsalar sauyin yanayi ta kunno kai, abin da ya kara ta'azzara al'amura. A bayyane yake abin na shafar mu, ga misali a yanayin karancin ruwan da ambaliya da tsananin zafi da fari."

Turai na fuskantar tsananin zafin cikin hanzari, fiye da kowacce nahiya. Jamus na zaman guda daga cikin yankunan da ke fuskantar karancin ruwa a duniya, inda tuni matsalar ta bayyana. Ga misali a yanzu haka ruwan da ke kogin Elbe ya yi karanci, inda zirga-zirgar jiragen ruwa ba ta yiwuwa.

Sannan akwai kudancin Turai, inda a lokacin bazara kimanin kaso  70 cikin 100 na al'ummar yankin ba sa samun isasshen ruwa. A Spaniya ga misali, ana fuskantar matsala a harkokin noma da yawan bude idanu. A shekara ta 2023 kusan mutane miliyan tara aka tilasta takaita amfani da ruwa, yankin Andalusia da ke kudancin abin ya fi shafa. Abin da kwararre a fannin ruwa a cibiyar kula da muhalli ta Turai Moroz tilas fa sai an samo maganin matsalar daga tushe:

Rijiya a Spain cikin kamfar ruwaHoto: DW

"Mafi yawan ruwan da ake samu yana zuwa ne ba daga dan Adam ba, kamar famfuna. Saboda haka kafin mu shiga gadan-gadan kan yadda za mu takaita amfani da ruwa a gidaje da ma'aikatu da wuraren linkaya da gonaki, ya kamata mu tabbatar mun shawo kan matsalar daga tushe, ma'ana mu kare muhallinmu."

Fari a IngilaHoto: Oli Scarff/AFP

Kimanin kaso 71 cikin 100 na duniyarmu a lullbe yake da ruwa, amma kaso uku ne kacal tsabtatacce. Sauran kankara ce da kuma wanda ke binne can kasan karkashin kasa, kuma ga kaso daya kacal dan Adam ke iya kai wa. KImanin kaso 70 cikin 100 na wannan kaso dayan, ana amfani da shi a fannin aikin gona, sauran kuma a raba tsakanin masana'antu da gidajen jama'a. Sai dai kuma dumamar yanayi, na barazana ga samuwar ruwan.