Turai za ta taimaka wa Kurdawan Iraki
August 11, 2014Talla
Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya fadi a wannan Litinin cewa kamata ya yi kasashen kungiyar Tarayyar Turai na EU, su amsa kiran Kurdawa 'yan Iraki na a tallafa wa mayakan su da kayan yaki dan tunkarar mayakan IS.
A cikin wata wasika da ya aike wa babbar jami'ar kula da harkokin wajen keatere ta kungiyar EU, Catherine Ashton, Fabius ya ce abu ne mai mahimmanci daga yanzu kasashen na Turai su tashi dan ba da wannan tallafi.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo