1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turjiyar gwamnatin Assad na Siriya

April 27, 2012

Majalisar Dinkin Duniya na zargin gwamnatin Siriya da sabawa yarjejeniyar da zata maido zaman lafiya a kasar, kasancewar dakarunta sun cigaba da luguden wuta

Smoke rises from the Al Qusoor district of Homs in this handout picture dated April 14, 2012. REUTERS/Waseem Al Qussoor/Shaam News Network/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya ce gwamnatin Siriya ta sabawa yarjejeniyar da ta amince da shirin sulhun da ya kamata ya kawo zaman lafiya a kasar, bayan da ta cigaba da ajiye dakarunta da manyan makamai a wasu biranen kasar. Shugaban Majalisar Dinkin Duniyan ya ce yana cike da damuwa dangane da irin rahotannin bude wutan da ake yi a biranen da ke da yawan al'umma.

Tawagar Majalisar Dinkin Duniyan ta je ta ganewa idanunta wani wurin da wasu bama-bamai suka tarwatse, abunda ya kai ga faduwar wani bene ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane 16, a yayin da gwamnati da 'yan adawa suka yi ta dora wa juna alhakin wannan ta'asa.

Yarjejeniyar tsagaita wutan da ya kamata ya fara aiki tun ran 12 ga watan Afrilu bai yi wani tasiri ba,kuma kawo yanzu, kasashen yamma sun yi barazanar daukar matakin soji idan har lamura basu canza ba kamar yadda ministan harkokin faransa Alain Juppe ya bayyana:

"Ko dai shirin Kofi Annan ya yi aiki ko da ya yi. Idan bai yi ba ba zamu cigaba da kawar da kai ga abubuwan da gwamnatin Damaskus ke yi ba, idan har bata yi amfani da kuduri ko daya daga kudurori shidda na shirin ba dole ne mu dauki wani mataki"

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala