Turkawa dubu 40,000 sun fita zanga-zanga a Jamus
July 31, 2016Dubban magoya bayan shugaba Recep Tayyip Erdogan sun gudanar da zanga-zanga tare da nuna adawa da masu yunkurin juyin mulki da ya gaza nasara a kasarsu ranar 15 ga watan nan na Yuli. Wannan zanga-zanga dai ta birnin Colgne ta wakana cikin matakan tsaro saboda fargaba ta barkewar tashin hankali.Masu zanga-zangar dauke da tutar kasar ta Turkiyya sun fara wannan zanga-zangar da taken kasar ta Turkiyya da ma na nan Jamus. Kuma yawan wadanda suka fito zanga-zangar sun kai kimanin dubu 40,000 a cewar 'yan sanda.Kevset Demir, na daga cikin wadanda suka fita wajen wannan zanga-zanga:
"Nazo nan wurin ne dan ina adawa da yunkurin juyin mulki a Turkiyya ko da yake akwai masu cewar nuna goyon bayan Erdogan muka fito, ba haka ba ne mu dai muna adawa da duk wani yunkuri na soja na kifar da gwamnatin farar hula. Da yawa sun fito ne dan kare dimokradiyya da kare hakkin bil Adama."