Turkiya: An cafke wanda ake zargi da kai harin Santanbul
January 17, 2017Talla
A cewar kanfanin dillancin labaran kasar ta Turkiya na Anadolu, wanda ake tuhumar sunan shi Abdulgadir Masharipov, sai dai kuma a cewar kanfanin dillancin labarai na Dogan mutumen na amfani da sunan Abou Mohammad Khorassani a matsayin sunansa na badda sawu a cikin kungiyar IS.
Shi dai Abdulgadir Masharipov mai shekaru 34 da haihuwa, an kamashi ne ya yin da yake tare da dansa mai shekaru hudu a wata Unguwa ta birnin Santanbul bayan da aka gudanar da wani babban binciken 'yan sanda a cewar tashar talbijin ta kasar ta TRT. Tun dai da kwanaki uku ne 'yan sanda na Turkiya suka gano maboyarsa, amma kuma suka yi ta bin shi domin gano abokan tafiyarsa.