Tsare wasu lauyoyi a Turkiya
March 16, 2016![Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan](https://static.dw.com/image/19111830_800.webp)
Talla
Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyan ya sanar da cewa zai fadada ma'anar ta'addanci a kasar, inda zai hadar da malaman makarantu da jami'oi da kuma 'yan jarida da ma 'yan adawar kasar. Tsare wadannan lauyoyi dai ya biyo bayan cafke wasu malaman makaranta guda uku a Turkiya bisa zarginsu da farfagandar ayyukan ta'addanci da aka yi a jiya Talata. Su dai malaman an kama su ne bayan da suka sanya hannu kan wani koke da ke yin tir da matakan da sojojin kasar ke dauka a kan jam'iyyar Kurdawa ta PKK a kasar.