Turkiya: Gyara ga kundin tsarin mulki
March 27, 2017![Kuri'ar yin gyara ga kundin tsarin mulkin Turkiya](https://static.dw.com/image/38124114_800.webp)
In har sakamakon kuri'ar raba gardamar ya amince da yi wa kundin tsarin mulkin Turkiyan kwaskwarima, hakan zai ba wa Shugaba Recep Tayyip Erdogan damar fadada ikonsa. A nan Jamus 'yan kasar ta Turkiyya su kimanin sama da miliyan guda da suka cancanci kada kuri'a, za su sauke wannan nauyi a kananan ofisoshin jakadancin kasar da ke fadin Jamus. A can Turkiyya a ranar 16 ga watan Afrilu za a kada kuri'ar raba gardamar a kan kwaskware kundin tsarin mulkin. Wata takaddama a kan gangamin yakin neman zabe da 'yan siyasar Turkiyya a Jamus suka so yi, ta janyo tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu lamarin da ya sa Shugaba Erdogan ya soki Jamus da bin manufofin 'yan Nazi, kalaman kuma da 'yan siyasa a Jamus din da ma nahiyar Turai suka yi tir da su.