Shugaban jaridar Cumhuriyet ta Turkiya ya shiga hannu
November 11, 2016A makon da ya gabata 'yan jari guda tara ne na jarida ta Cumhuriyet aka kama cikin su har da babban editan jaridar Murat Sabuncu, inda aka tsare su bisa zargin su da ake da hannu a cikin ayyukan ta'addanci a kasar ta Turkiya.
Ofishin babban mai shigar da kara na Gwamnatin ta Turkiya ya sanar cewa, wannan kamu an yi shi ne bisa bincike da ake yi kan ayyyukan ta'addanci, ta hanyar gama baki da masu goyon bayan babban Malamin nan Fethullah Gülen, wanda hukumomin na Turkiya ke zargi da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba na ranar 15 ga watan Yuli da ya gabata.
Sai dai masu fafutikar kare hakin dan Adam, da sauran masu adawa da manufofin shugaban na Turkiya, na ci gaba da sukar wannan mataki, inda suke zargin gwamnatin da saka tarnaki wajen incin fadar albarkacin baki.