Turkiya ta bayyana dakatar da tura dakaru zuwa Iraki
December 8, 2015Talla
Gwamnatin kasar Turkiya ta dakatar da tura sojoji cikin yankin arewacin kasar Iraki, amma ta ce ba ta tsara shirin fara janye dakaru ba. Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar da haka bayan mahukuntan Iraki sun nemi yanje dakarun Turkiya da aka tura kusa da yankunan da ke hannun tsagerun kungiyar IS masu neman kafa daular Islama.
Ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu ya tabbatar da wannan mataki lokacin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Iraki Ibrahim al-Jaafari. Tuni Firaminista Ahmet Davutoglu na Turkiya ya ayyana niyar kai ziyara zuwa Iraki nan gaba kadan, domin kawo karshen sabanin da aka samu tsakanin kasashen biyu.