Turkiya ta ja kunnen Kungiyar EU kan mutunta yarjejeniya
April 7, 2016Talla
.Shugaban Turkiyan a yayin wani jawabi gaban wani taro a Ankara yayi nuni da cewar.
''Akwai ka'idoji ko hanyoyin da yakamata abi kuma a kwai wasu sharuda,idan dai kungiyar EU ta kasa daukar matakan da yakamata ta dauka ko ta gaza cika dukkanin alkawarurrukan da ta yi,to Turkiya ma ba za ta martaba yarjejeniyar ba.''
Tun dai a watan Maris ne aka cimma yarjejeniyar tare da zayyana matakan da za a bi wajen dakile kwararar 'yan gudun hijira zuwa Kasashen Turai a inda Turkiya ta amince da karbar 'yan gudun hijirar da suka futo daga kasar Girka abisa sharadin samun tallafin Euro Biliyan 6 daga hannun Kungiyar.