1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta kai farmaki cikin ƙasar Siriya

October 4, 2012

Bisa ga dukkan alamu ƙasashen Turkiya da Siriya na daɗa shiga yaƙi da juna.

A Turkish Air Force F-4 war plane fires during a military exercise in Izmir, in this May 26, 2010 file photo. Turkey lost a F-4 warplane, similar to the one pictured, over the Mediterranean on June 22, 2012, but Turkish Prime Minister Tayyip Erdogan said in his first public comments, he could not say whether the plane had crashed or been shot down. REUTERS/ Osman Orsal/Files (TURKEY - Tags: MILITARY CIVIL UNREST TRANSPORT POLITICS)
Jirgin yaƙin TurkiyaHoto: REUTERS

An bada rahotannin cewa ƙasar Turkiya ta ƙaddamar da farmakin soji cikin ƙasar Siriya bayan wasu rokokin da Siriya ta harbo sun hallaka mutane biyar dake cikin ƙasar ta. An dai zargi sojin gwamnatin Siriya da harbo rokokin. Wata sanarwa daga ofishin Firimiyan ƙasar Turkiya Tayyep Erdogan tace, irin wannan tsokalar nan gaba ba za a riƙa barinta ba tare da martani ba. Ƙasar Turkiya da ƙungiyar NATO sun amince da gudanar da wani taron gaggawa kan lamarin. Ƙasar Turkiya dai a hukumance ta nemi MDD da ta tsawata wa Siriya, yayinda ita kuwa ƙungiyar tsaron NATO ta fidda sanarwar yin Allah wadai da harin na ƙasar Siriya.

A cikin ƙasar ta Siriya kuwa an bada rahotannin cewa wasu tagwayen hare-haren bam a birnin Aleppo sun hallaka aƙalla mutane 100 a jiya Laraba, amma fa inji wata ƙungiya dake zama a can birnin birnin London dake lura da abinda ke faruwa a ƙasar Siriya. Wata ƙungiyar leƙen asiri ta ƙasar Amirka kuwa tace ƙungiyar AL-Nusra-Front itace ta ɗauki alhaƙin kai harin. An dai kai harin a inda gwamnati ta fi ƙarfi, ko da yake yanzu birnin Aleppo ya kasu tsakanin masu neman kifar da gwamnati da ita gwamnatin kanta.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal