Turkiya za ta dakatar da dokar kare hakki
July 21, 2016Kasar Turkiya za ta bi sahun Faransa na dakar da shirin amincewa da yarjejeniyar Kungiyar Tarayyar Turai kan dokokin kare hakkin bil Adama zuwa wani dan lokaci bayan da kasar ta kafa dokar ta-baci kamar yadda mataimakin firaministan kasar Numan Kurtulmus ya bayyana wa kafar yada labarai ta NTV a ranar Alhamis din nan.
A yammacin Laraba ne dai Shugaba Tayyip Erdogan ya bayyana cewa kasar ta Turkiya za ta kasance karkashin dokar ta-baci tsawon watanni uku bayan yunkuri na soja su karbi mulkin kasar, abin da a cewar Shugaba Erdogan zai taimaka wajen ganin wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin sun gurfana a gaban kuliya.
Kasar Faransa dai ta sanya dokar ta-baci bayan harin ta'addanci da aka kai a watan Nuwamba na bara a birnin Paris.
A cikin jawaban na Kurtulmus ta kafar yada labaran NTV ya ce wannan dokar ta baci za ta sanya a tattauna da wadanda ake zargi kai tsaye cikin lokaci, sannan akwai shirin yin kwaskwarima a rundinar sojan kasar.