Turkiya za ta inganta dangantaka da Afirka
December 24, 2017Erdogan ya fadawa taron manema labarai a birnin Ankara cewa ya dauki sake inganta dangantaka da kasashen Afirka da muhimmancin gaske, kuma Turkiya na son bude ofishin jakadancinta a dukkanin kasashen Afirka.
Ya kuma yi jinjina da godiya ga Shugaba Omar al-Bashir na Sudan din saboda halartarsa taron koli da aka yi a Istanbul kan Birnin Kudus bayan da Shugaba Donald Trump ya bayyana birnin a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.
Shi dai Shugaba Al-Bashir na da sammacin kasa da kasa a kansa a kotun da ke hukuntan masu manyan laifuka ta ICC saboda zargin kisan kiyashi da haddasa yaki a Sudan.
A lokuta da dama dai Erdogan ya sha kira ga kasashen na Afirka su rufe makarantu da ke karkashin Fethullah Gulen, malamin addinin Islama nan da ke zaune a Amirka saboda zarginsa da hannu a yunkurin kifar da gwamnatinsa.