1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurkiyya

Turkiyya: An tsare lauyan Imamoglu

Abdullahi Tanko Bala
March 28, 2025

An tsare mutane kusan 1,900 a ci gaba da zanga zangar adawa bayan kama magajin garin Istanbul Ekrem Imamoglu

Jagoran adawa a Turkiyya Ekrem Imamoglu
Jagoran adawa a Turkiyya Ekrem ImamogluHoto: Ozan Kose/AFP

Magajin garin Isantanbul Ekrem Imamoglu ya ce hukumomi sun kama lauyansa inda ake ci gaba da tsare shi.

Ya wallafa a shafinsa na X cewa an tsare lauyansa Mehmet Pehlivan bisa wasu dalilai da ba a fayyace ba.

Pehlivan ya wakilci Imamoglu a kotu a ranar lahadi kan zargin da ake yi masa na cin hanci.

Imamoglu ya kasance babban abokin hamaiyyar shugaba Recep Tayyip Erdogan, kuma an kama shi ne a makon da ya gabata yan sa'oi kafin ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa, lamarin da ya haifar da gagarumar zanga zanga da aka dade ba a gani ba a Turkiyya cikin shekaru goma da suka gabata.

Tun daga wannan lokaci hukumomin Turkiyya sun kama mutane kimanin 1,900 da suka hada da masu zanga zanga da kuma yan Jarida.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW