1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta yi barazanar kai hari Arewa maso gabashin Siriya

Zulaiha Abubakar
October 5, 2019

Shugaba Receep Tayyip Erdorgan na Turkiyya ya yi barazanar kai farmakin sojoji Arewa maso Gabashin kasar Siriya, yankin da Amirka ta jibge dakarunta masu aikin kwantar da tarzoma.

Turkey Explosion
Hoto: picture alliance/AP Photo/Yasin Bulbul/Presidential Press Service


Wannan gargadi na zuwa ne bayan rushewar yarjejeniyar da Turkiya da Amirka suka kulla kan tsaron iyakokin kasar ta Siriya, a watan satumbar da ya gabata ne dakarun sojin Turkiyya suka fara aikin jibge makamai a yankin Sanliurfa da ke Kudu maso Gabashin kasar ta Siriya bayan shugaba Erdorgan ya bayyana takaici game yan kafar da  Amirka ta ke yi a aikin tsaron hadakar.

 

A baya bangaren Kurdawan masu yaki da mulkin shugaba Bashar al-Assad na Siriya sun bayyana gamsuwa da hadin gwuiwar Amirka da Turkiyya don maido da zaman lafiya a yankin.