Turkiyya da Amirka na shawarar ceto 'yan Siriya
October 7, 2019Talla
A wata zantawar da suka yi ta wayar tarho, Shugaba Racep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya tare da shugaban Amirka Donald Trump, sun tattauna kan yiwuwar samar da tuddan mun tsira a yankin arewacin kasar Siriya.
Zantawar shugabannin biyu dai na zuwa ne bayan wasu kalaman da shugaban Turkiyyar ya yi na cewar babu makawa sojoji za su afka wa arewacin na Siriya.
Kasar dai ta zargi Amirka ne da fari da kokarin yin kafar angulu ga shirin samar da tuddan mun tsiran a yankin na Siriya, inda Turkiyyar ke shirin ajiye Siriyawa akalla miliyan biyu.
A share guda kuwa, fadar shugaban kasa a Turkiyyar, ta ce Shugaba Erdogan zai ziyarci fadar White House ta Amirka cikin watan gobe, bayan gayyatar da shugaban Amirkar ya yi masa.