Khashoggi :Shirin binciken kasa da kasa
December 11, 2018Ministan harakokin wajen kasar ta Turkiyya Mevlüt Cavusoglu ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai a wannan Talata a birnin Ankara, ya kuma yi karin bayani a game da dalillansu na daukar wannan mataki yana mai cewa:
"Mutanen da suka aikata wannan laifi a gaban kotun Turkiyya ce ya kamata a gurfanar da su, to amma Saudiyya ta kiya. A kan haka ne muka tattauna da Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya da wasu manyan kasashe kan yiwuwar gudanar da bincike na kasa da kasa kan lamari"
Minista Cavusoglu ya ce a daura da taron G20 ne da ya gudana a farkon wannan wata na Disamba a ya tattauna da wasu takwarorinsa na kasashen duniya da suka hada da kasar Kanada kan wannan batu inda suka ye suna son yin baki guda wajen shigar da wannan bukata.