1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Turkiyya da Saudiyya na yunkurin inganta alaka

Abdoulaye Mamane Amadou
February 3, 2026

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan na ziyarar farko a Saudiyya cikin shekaru biyu inda hulda ta

Shugaban Turkiya a lokacin da ya sauka a birnin Riyad na kasar Saudiyya
Shugaban Turkiya a lokacin da ya sauka a birnin Riyad na kasar SaudiyyaHoto: Mustafa Kamaci/Turkish Presidency/Anadolu Agency/IMAGO

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya isa birnin Riyadh a ziyararsa ta farko a Saudiyya cikin tsukin shekaru biyu, a daidai lokacin da ake hasashen ksashen biyu na kara kusantar juna bayan dogon lokaci na zaman doya da manja.

Saudiya: Za a sanya takunkumi kan kadarorin Yarima

Dangantakar Turkiyya da Saudiyya ta ci gaba da ingantawa a ’yan shekarun nan, inda kasashen ke aiki tare kan muhimman batutuwan da suka shafi siyasar duniya da diflomasiyya, ciki har da goyon bayan Gaza da tallafa wa sabuwar gwamnatin Siriya bayan kifar da Bashar al‑Assad a shekarar 2024.

Sabon babi a binciken kisan Khashoggi

A ziyarar ta Shugaba Erdogan, ana sa ran zai yi tozali da yariman Saudiyya Mohammed bin Salman, sai dai kuma ba bayyana takamaiman batutuwan tattaunawa da za su tattauna ba, ko da yake kafofin gwamnatin Turkiyya sun ce shugaban Turkiyya da Yarima Salman za su tattauna ne kan yadda za su zurfafa huldarsu