1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun mutu a Tekun Turkiyya

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 26, 2019

Rahotanni daga Turkiyya na nuni da cewa wasu 'yan gudun hijira bakwai sun rasa rayukansu sakamakon nutsewar da jirgin ruwan da suke ciki ya yi a Tekun Van da ke gabashin Turkiyya.

Türkei Bootsunglück auf dem Van See
Jirgin ruwa dauke da 'yan gudun hijira ya kife a TurkiyyaHoto: picture-alliance/AA/H. Nacar

Masu ayyukan ceto sun nunar da cewa sun samu nasarar ceto wasu 'yan gudun hijira 64 a Tekun na Van. 'Yan gudun hijirar da ke cikin jirgin ruwan dai sun fito ne daga kasashen Afganistan da Pakistan da kuma Bangaladash. Tekun na Van na kimanin nisan kilomita da 100 da kan iyakar Turkiyyan da Iran. Mafi akasari 'yan gudun hijirar na fito wane daga kasashen da ke makwabtaka da Turkiyyan ta kan iyakoki, a kokarinsu na tsallakawa kasashen Turai da suke wa kallon tudun mun tsira.